Shugaba Kim Jong Un na kasar Koriya Ta Arewa ya sake fitowa bainar jama’a, bayan sake kaurace wa jama’a da ya yi na tsawon makonni uku a jere, kamar yadda ya yi a baya har ake ta rade-radin cewa ya na fama da rashin lafiya ko ma ya mutu.
Kafar yada labaran gwamnatin kasar, yau Lahadi, ta ce Shugaba Kim ya jagoanci wani taro wanda ya tattauna kan batun fadada abin da ya kira, “Ayyuakan tauna tsakuwa ta wajen amfani da karfin nukiliya.”
(Jirgin yakin Amurka samfurin B-52 mai daukar makamin nukiliya wanda ta kan gargadi Koriya Ta Arewa da shi)
Hotunan sun nuna yadda Shugaba Kim ya yi ta rattaba hannu kan wasu kundodi, da yin jawabai, da kuma nuna yatsa a wani hoton talabijin din da aka jirkita shi saboda badda da sawu.
Hotunan, wadanda aka wallafa su a kafafen yada labaran gwamnatin kasar, ba su nuna wata alamar rashin lafiya tattare da Kim ba.
Wannan shi ne karon farko da Kim ya fito bainar jama’a tun daga ranar 1 ga watan Mayu, lokacin da ya bayyana a wani bukin bude wani kamfanin yin takin zamani, bayan an shafe makonni uku ba a gan shi ba a bainar jama’a.