Shugaba Joseph Kabila, Na Da Niyyar Mutunta Kundin Tsarin Mulkin Kasar Kwango

Shugaba Joseph Kabila

kakakin gwamnatin Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango, ya ce, shugaba Jospeh Kabila, na da niyyar ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar tare da shirin mika mulki bayan an kammala zabe

Wani kakakin gwamnatin Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango, ya ce, shugaba Jospeh Kabila, na da niyyar ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar tare da shirin mika mulki bayan an kammala zabe, kamar yadda aka tsara za a yi a watan Disamba.

Yayin wata ganawa da ya yi da sashen Faransanci na Muryar Amurka, Lambert Mende, ya ce duk da jinkirin da ake samu, gwamnati na kokarin kammala shirya rijistar masu kada kuri’a a yankunan karkara, kuma za a yi zaben kamar yadda hukumar zaben ta tsara.

Kakakin ya kara da cewa, shugaba Kabila ba shi da niyyar sake tsaya wa takara, sannan a watan Yuli zai bayyana zabinsa na dan takarar da zai nemi maye gurbinsa a zaben na watan Disamba.

Kamar dai yadda kundin tsarin mulkin kasar ta Congo ya tanada, ba a amince shugaban kasa ya tsaya takara a wa’adi na uku a jere ba.

A watan Janairun 2001, shugaba Joseph Kabila ya karbi mulkin kasar, bayan da aka kashe mahaifinsa Laurent Kabila.

Sannan an zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekarar 2006 aka kuma sake zaben shi a shekarar 2011 a wa’adi na biyu.