Shugaba Jonathan Yayi Alkawarin Yin Zabe Mai Adalci

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Jiya aka bude taron koli na shugabannin kasashen Afirka da gwamnatin Amurka. Yayin da yake jawabi a ofishin jakadancin Najeriya a nan Amurka shugaban Najeriya ya tabo batutuwa da dama sabili da haka wakilin Muryar Amurka ya zanta da mataimakin jakadan Najeriya akan abubuwan da shugaban ya fada

A zantawarsu da mataimakin jakadan Najeriya a nan Amurka Alhaji Habibu Habu sun yadda cewa taron yayi armashi.

Shugaban Najeriya Jonathan yayi maganganu da yawa. Yayi maganar zaben da ya faru na baya da kuma zaben gaba. Alkawarin da ya yiwa mutane a wancan lokacin ya cika. Yayi misali da asarar jihar Edo da jam'iyyarsa tayi ya kuma gayawa mutane su yi hakuri, su rungumi kaddara. Mutane sun ji dadin cewa PDP zata yi asarar jiha ta kuma hakura.

Abun da shugaban yace tamkar manuni ne ga zabe mai zuwa domin yace idan zabe yayi kyau, wato an yi shi da adalci zai amince da sakamakon. Ya fada karara cewa idan ya ci zabe ya ci idan kuma bai ci ba shi zai koma kauyensa ya zauna. Idan ya ci zai yi murna. Idan kuma bai ci ba zai yi murna muddin yayi zabe mai kyau.

An yiwa shugaban Najeriya tambayoyi da yawa kamar batun ayyuka da gidaje da dai sauransu amma babu tambaya akan harkar tsaro.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Jonathan Yayi Alkawarin Yin Zabe Mai Adalci - 2' 07"