Da yaka jawabi tunda farko mai masaukin baki, Gwamna Mu'azu Babangida Aliyu na jihar Neja yayi shagube ne ga wadanda suka sauya sheka daga jam'iyyar PDP. Yana cewa shi karkashin inuwar PDP aka zabe shi, da sauya sheka, da tuni yayi murabus.
Shi kuma a nasa jawabin, Shugaba Goodluck Jonathan yayi magana ne kan irin mashahuran mutane da asalinsu daga jihar Neja. Mr. Jonathan yace tsohon shugaban Najeriya na farko mashahurin dan Afirka Dr. Namdi Azikwe, da tsohon dan tawaye Odumegu Ojukwu, da Janar Ibrahim Badamasi Babangida, da Janar Abdulsalami Abubakar duk an haifesu a jihar Neja.
Shugaba Jonathan wanda ya ziyarci tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma sarkin Minna Alhaji Umar Farouk Bahago.
Sai dai shugaban kasar bai yi magana kan matsalolin tsaro da kasar take fuskanta ba.
Ga rahoto.
Your browser doesn’t support HTML5