Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya soke shirin zuwa garin Chibok.
WASHINGTON, DC —
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya soke shirin zuwa garin Chibok, inda ‘yan Boko Haram suka saci dalibai mata ‘yan makaranta su fiye da 200 a watan da ya shige.
Jami’ai sun fada a yau jumma’a cewa Mr. Jonathan ya kasa zuwa Chibok dake Jihar Borno a saboda dalilai na tsaro.
A yanzu shugaban na Najeriya zai wuce zuwa Paris a Faransa domin wani taron kasashe makwabtan Najeriya da shugaba Francoise Hollande ya kira. Su ma shugabannin kasashen Benin, Kamaru, Nijar da Chadi zasu halarci taron.
A nan Washington, darekta mai kula da harkokin Afirka a ma’aikatar tsaron Amurka, Alice Friend, ta fadawa wani kwamitin majalisar dattijai cewa Najeriya ba ta da suna mai kyau kan batun yaki da Boko Haram.