Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ya ziyarci tsohon shugaban Nigeria Janaral Ibrahim Babangida a Minna.
Wakilin sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari ya aiko da rahoton cewa, masu nazarin harkokin siyasa sunce ziyarar ba zata rasa nasaba da neman goyon bayan tsohon shugaban ba, a yayinda zaben shekara ta 2015 ya karato.
Tsohon gwamnan jihar Kano da Benue a zamanin mulkin soja, Kanal Aminu Isa Kontagora yace ana bukatar irin wannan tuntunba tsakanin shugabanin domin ana cikin siyasa ga kuma matsalar tsaro a kasar. A saboda haka dole an san cewa wadannan batutuwa za'a tautauna.
Shi kuma, shugaban kwamitin labarai a Majalisar wakilan jihar Niger, Bello Azara yace ya kamata ace tun da dadewa anyi irin wannan tattaunawa. Yace mutane zasu zavi cewa kila doin shugaba Jonathan yana neman goyon baya domin yaci zabe, in ba haka ba, mai yasa sai yanzu ne za'a yi irin wannan ganawa.
Your browser doesn’t support HTML5