Shugaban kasa Goodluck Jonathan na shirin ganawa da iyayen ‘yan matan da aka sace a chibok gobe 21 ga watan nan a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja. Yau litinin iyayen zasu hallara a fadar shugaban kasa.
A hirar da aka yi da daya daga cikn iyayen wadanda aka sace, Mr. Amos, ya ce tun farko da aka fara zancen shugan kasa na so ya gana da iyayen ‘yan matan, hakan bai yiwu ba, don, gwamnatin jiha ta ce ta gaya masu cewa wadanda a ‘yayansu suka gudo kawai ake bukatar gani. Wannan wani abin mamaki ne domin a ganin Mr. Amos, su da 'yayansu ke chan a tsare, suke bukatar ganawa da shugaban kasa fiye da kowa.
Yanzu an yarda iyaye 114 su gana da shugan kasar daga bangaren wadanda suka sami ‘yayansu da wadanda basu samu ba.
Mr. Amos ya kara da cewa, ya yi mamaki yadda tun lokacin da abin ya faru babu wani daga gwamanti da ya zo ya jajantamasu ko ya gana da su, sai dai su da kansu iyayen suke neman mafita.
Ya ci gaba da cewa, su dai iyaye suna rokon gwamnatin shugaban kasa da ta taimaka ta ceto rayukan ‘yayansu lami lafiya.
Your browser doesn’t support HTML5