Shugaba Goodluck Jonathan ya sake fadin cewa babu abinda zai hana ayi zabe a Nigeria

Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria

Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ya tabbatar cewa babu abinda zai hana yin zabe a Nigeria.

Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ya tabbatar cewa babu abinda zai hana yin zabe a kasar.

Shugaban ya bada wannan tabbacin ne lokacinda yake kaddamar da wasu jiragen ruwan yaki guda hudu a birnin Ikko.

Shugaban yace hare haren 'yan kungiyar Boko Haram ba zai hana yin zabe a Nigeria ba. Yace sojojin Nigeria a shirye suke, zasu yaki yan Boko Haram tare da maida zaman lafiya a ko ina a duk fadin Nigeria.

Haka kuma yace, an fara samun nasarar murkushe yan Boko Haram, a saboda haka ba abinda zai hana ayi zabe a Nigeria. Shugaba Jonathan yayi kira ga 'yan Nigeria da su baiwa sojoji goyon baya domin ganin an samu nasara a yakin da ake yi da 'yan tawaye.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Jonathan yace babu abinda zai hana ayi zabe a Nigeria