Shugaba Donald Trump yayi gargadin cewa “Zai zama ranar bacin rai ga Koriya ta Arewa” Idan har Amurka ta dauki matakin soja akan ta.
Shugaban yayi wannan batu ne lokacin da yake tare da Sarkin Kuwait, Sheik Sabah al-Ahmad Al-Sabah, inda yake amsa tambayoyin manema labarai, ya kara da cewa “Muna fatan baza ta kaimu ga amfani da sojojin mu ba a akan Koriya ta Arewa.”
Trump yaki amsa tambayar ko za’a iya amincewa da Koriya ta Arewa ta cigaba da aje Makamanta na Nukiliya amma a cigaba da lallashinta har sau biyu.
Trump ya tsaya tsayin daka kan rayin shekaru 25 a baya gwamnatin Amurka ta gane cewar “Kwana daya bayan cimma yar jejeniya, Koriya ta Arewa ke cigaba da shirinta na makamin Nukiliya,”
Bayan maganganun na shugaban, wani babban jami’i a gwamnatin ta Trump ya bayyan damuwar cewar ba za’a iya lallamar Koriya ta Arewa ba.