Dazu dazun nan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda ya dawo daga jinya a Burtaniya, ya gabatar da jawabi.
Shugaba Buhari ya ce yayin da ya ke jinya ya na bin diddigin abubuwan da ke faruwa akasar. Ya ce ya ji takaicin wasu furuce furuce musamman ma a kafafen sada zumunci. Ya ce kowani dan Najeriya na da 'yancin zama inda ya ga dama ba tare da wata tsangwama ba.
INSERT BUHARI' ACTUALITY
ACT:- Nigeri's unity is settled and not negotiable----------
VOICE: Yace, "Batun zaman Najeriya dunkulalliyar kasa abu ne da aka rika aka tsai da shawara akai kuma ba za a sake warwarewa ba. Ba za mu bar wasu marasa mutunci su su tayar ma na da wata rigima ba; kuma da zarar abubuwa su ka rincabe su tsere su bar wasu da aikin maido da kwanciyar hankali, watakila da ta wajen zubar da jininsu"
"Kowane dan Najeriya na da damar rayuwa da kuma gudabar da harkokin kasuwancinsa a ko'ina a Najeriya ba tare da wani cikas ba." Shugaban yaci gaba da cewa
Ga Ibrahim Ka'almasiu da cikakken bayani
Your browser doesn’t support HTML5