Shugaba Buhari ya yi Alkawarin Hukunta Masu Laifi

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amshi sakamakon binciken komitin da ya kafa ya gudanar da bincike a kan makudan kudaden da aka gano a gidan tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasa Ambassador Ayo Oke da suka kai dala miliyon 43.

Komitin da shugaban Muhammadu Buhari ya kafa ya binciki kudaden da aka gano a gidan dake anguwar Osbone Towers a jihar Legas karkashin jagoranci Ambassador Babagana Kingibe yana da wakilan da suka hada da tsofaffin darektocin hukumar leken asiri irin su, Ambassador Zakari Ibrahim da Ambassador Ezekiel Oladeji da Cif Albert Onson da suka taimaka wurin fidda wannan rahoton.

Shugaban Buhari ya baiwa al’ummar kasa tabbacin cewa babu wani abin da za a boye a wannan bincike, saboda duk wanda ke da hannu a wannan badakalar zai fuskanci shari’a. Shugaban yace gwamnati zata bi dokokin kasa wurin aiwatar da wannan sakamkon bincike da aka gabatar masa.

Da yake Karin haske a kan bayanan shugaban kasa, Mallam Garba Shehu kakaki a fadar gwamnatin Najeriya, yace duk wani mai laifi ko wanda aka samu hannunsa a wannan badakalar sai an yi maganin shi kuma sai ya amsa laifin shi, amma kuma za a yi hakan ne bisa dokokin da suka kafa wadannan hukumomi.

Your browser doesn’t support HTML5

BUHARI REPORT