Shugaba Buhari Ya Tabbatarwa 'Yan Najeriya Zabe Cikin Lumana

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce za a tabbatar da tsaro a rumfunan zabe gobe Asabar a lokacin da za a gudanar da babban zabe a kasar, mako daya bayan da aka dage zaben.

A wani jawabi da ya yi wanda aka nuna ta talabijin a fadin kasar yau Jumma’a, Shugaba Buhari ya ce an dauki matakan tsaro a fadin kasar don zaben, ya kuma tabbatar da cewa mutane zasu kada kuri’a ba tare da wani fargaba ba.

Rikicin siyasa na zafafa a kasar yayin da ‘yan Najeriya ke shirin zaben sabon shugaban kasa da ‘yan majalissu. A lokacin yakin neman zaben su, jam’iyyar APC ta shugaba Buhari da babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun zargi juna da yinkurin yin magudi don canza sakamakon zabe.

A farkon makon nan ne shugaba Buhari ya kira ga sojojin kasar akan su dauki tsattsauran mataki akan duk wanda yayi yinkurin yin katsalandan a lokacin zaben.

Wadannan kalaman da shugaba Buhari yayi sun janyo suka mai zafi daga abokin takarar sa, Atiku Abubakar, wanda ya ce sojoji ba su da rawar da zasu taka wajen gudanar da zabe.