Shugaban ya gayawa gwamnonin cewa kasashen waje, musamman na yammcin turai da Amurka sun yi masa alkawarin ba da hadin kansu domin hakarsa ta cimma ruwa.
To saidai duk da wannan manufar alamar tambaya nan ita ce shin ina shugaba Buhari zai fara gnin cewa almubazaranci, wawura, da cin hanci da rashawa tamkar sun zama ruwan dare gama gari a Najeriya musamman a karkashin gwamnatin da shugaba Buhari ya gada.
A wata tattaunawa da wakilin Muryar Amurka ya yi da Alhaji Sani Aminu Dutsinma masanin tattalin arziki kuma dan siyasa da Alhaji Abubakar Ali mai fafutika da yaki da cin hanci da rashawa sun bayyana ra'ayoyinsu akan yadda shugaban zai cimma manufarsa.
A ganin Alhaji Abubakar Ali shugaba Buhari ya sakar ma hukumar EFCC mara ta samu ta yi aikinta yadda ya kamata ba sani ba sabo. Yace gwamnatocin da suka shude sun hanasu aiki. Shugaba Buhari ya sakar masu mara ya kuma kara masu karfin gwiwa su cigaba da yaki. Abu na biyu shugaba Buhari ya gaggauta ya toshe duk hanyoyin da ake bi ana sata. Na uku ya nemi hadin kan bangaren shari'a da yin yaki da sata, cin hanci da rashawa. Duk wani bincike da EFCC zata yi idan an kai kotu sai a samu matsala.
Shi kuma Alhaji Sani Aminu Dutsinma yace shi yana ganin aiki ne mai sauki a wurin shugaba Buhari. Kowa ya san irin yadda shugaba ya bi da rayuwarsa haka kowa ke bi. Ya zo lokacin da aka hambarar da jamhuriya ta biyu ya yi gyara. A wannan karon ma zai gyara.
Dangane da kasashen turai ko zasu yadda kudaden da aka kai kasarsu a dawo da su Alhaji Sani yace kasashen suna bukatar abu a wurn Buhari saboda haka dole su taimakeshi. Misali yadda ake farautar masu kwarara zuwa turai ba zasu so 'yan Najeriya su fantsama kan hanyar zuwa turai ba. Zasu iya sakarwa Najeriya duk kudin satar da aka gano a kasarsu kuma ba zai damu tattalin arzikinsu ba.
Ga cigaban rahoton Hassan Umaru Tambuwal.
Your browser doesn’t support HTML5