Shugaban Najeriya yayinda yake mayarda martani akan sabbin hare-haren da Boko Haram ke kaiwa a yankin arewa maso gabashin kasar ya kira ga al'ummar yankin da su dinga sa ido akan 'yan ta'ada.
Kwanan nan 'yan ta'adan suka kai hare hare akan garuruwan Chibok, Gombi da kuma anguwar Dolari kusa da birnin Maiduguri. Yace dole jama'a su saido sosai tare da taimakawa jami'an tsaro da labaran siri saboda murkushe 'yan ta'adan gaba daya.
Shugaban ya kuma jajintawa wadanda hare haren suka rutsaa da su tare da bada tabbacin gwamnatinsa zata taimakawa duk wanda suke kwance asibiti.
Onarebul Ibrahim Batakal Hassan mataimakin shugaban kasa na musamman akan harkokin tsare tsare da cigaba ya yi karin haske. Yace shugaban kasa na yaki da abubuwa uku ne da suka hada da ta'adanci domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali.
Su ma 'yan majalisar dattawan tarayya sun ziyarci wadanda suke kwance a asibititocin Yolandomin jajantawa. Sanata Abdulaziz Nyako shi ya jagoranci 'yan majalisar. Yace kusan kowane wata sai sun ziyarci Adamawa bisa ga hare-haren da ake kawowa. Ya karfafa mutane yana cewa kada su gaji, su cigaba da yin hakuri da inganta tsaro har lokacin da Allah zai kawar da bala'in.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5