Shugaba Buhari ya karfafa batun daukan matakan tsaro

Shugaba Buhari na Nigeria da Paul Biya na Kamaru

Shugaba Buhari yayi la’akari da kyakyar dangantakar dake tsakanin Nigeria da Kamaru, a saboda haka yace tilas kasashen biyu sun hada kai wajen yaki da yan Boko Haram

Laraba Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya kai ziyara kasar Kamaru a wani yunkurin karfafa hadin kai wajen yaki da yan kungiyar Boko Haram kamar yadda ya kai ziyara kasashen Chadi da jamhuriyar Niger bayan ya dare kan ragamar mulki.

A jawabin daya gabatar a Kamaru, bayan da yayi la’akari da kyakyar dangantakar dake tsakanin Nigeria da Kamaru da kuma irin barnar da yan Boko Haram suke yi, Inda y ace sun kashe dubban mutane haka kuma sun sa dubban mutane rasa matsuguninsu da halaliyarsu, sun zama basu da komai.

Ya. Kuma yi la’akar da kokarin da kasashen biyu suke yi na yaki da wannan masifa, a saboda haka shugaba Buhari yaee tilas ne kasashen biyu ba zasu yi sake a aniyar da suka kudurta na kawar da wannan masifa dake kokarin kawar da yancin mu da kuma nasarorin da muka samu a kasashen mu da kuma yankin mu tare

Yace tilas Nigeria da Kamaru su yaki wadannan abokanan gaba wadanda hare hare da suke kaiwa ya jawo wa mutane wahala na jin kai.. Haka kuma shugaba Muhammadu Buhari ya lura da cewa cewa babu kasar da ita kadai zata samu nasarar murkushe yan Boko Haram.

A saboda haka domin samun nasarar wannan yaki, akwai bukatar hadin kan tare dukkan kasashen biyu da kuma kowa da kowa, mu hada karfi mu murkushe yan Boko Haram mu kawo karshen wannan ta’adanci da ake yiwa mutane mu.

Tunda farko shugaban na Nigeria ya nuna farin cikinsa ga kyakyawar tarbo da aka yi masa da shi da tawagarsa inda yace cewa bai yi mamakin irin kyakyauwar tarnon da aka yi kmasa ba, idan aka yi la’akari da kara yan kasar Kamaru da shugaban kasar Paul Biya daya baiyana a zaman dan uwansa.

Bugu da kari shugaba Buhari yayi amfani da ziyarar yana mai cewa bari yayi amfani da wannan dama a hukunce ya baiyana godiyar gwamnatin Nigeria da shugaba Paul Biya, a saboda mafaka da ya baiwa wadanda suka arcewa hare haren ‘yan book Haram akan gidajensu da kuma irin goyon bayan da kasar Kamaru take baiwa rundunar soja da sauran jami’an tsaron kasar.

Haka kuma ya yiwa iyalan wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa dasu jaje da ta’azya a Kamaru da kuma Nigeria.

Your browser doesn’t support HTML5

Jawabin shugaba Buhari a kasar Kamaru 3'58"