Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Yakin Neman Zabe

Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa a Abuja tare da wasu tare da wasu kusoshin jam’iyarsa ta APC mai mulkin kasar, inda shugaban kasar ya ya gargadi yan majalisar da suyi kampe a kan ‘ka’ida da manufa mai kyau ba tare da ‘batanci ko cin zarafin kowa ba.

Shugaba Buhari ya nada Bola Ahmed Tinubu jigo a jami’iyar APC matsayin wanda zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben tare da wasu masu fada aji a jam’iyar da aka baiwa mukamai dabam-dabam, kama dag gwamnoni da ‘yan majalisa da duk masu ruwa da tsaki a wurin samowa jami’iyar nasara a zaben dake tafe.

Wannan majalisar yakin neman zabe ita zata tsara hanyoyin da za a bi na neman kudade da gudanar da ayyuka da kuma tuntuba d daukar matakai da zasu kai jami’iyar ga samun nasara. A wurin kaddamarwar, shugaba Buhari ya dora Tinubu alhakin tabbatar da ganin ‘yan takarar APC tun daga shugaban kasa zuwa ‘yan majalisa sun samu nasarar a wannan zabe.

Shugaba Muhammadu ya bukaci majalisar ta tabbatar da tayi damarar yakin neman zabe bisa ka’ida na zabe ba tare da cin zarafi ko kawo tashin hankali da wasu fitintinu. Yana mai bada tabbacin cewa yanda aka gudanar da zabe na gaskiya da adalci da ya kawo shi a kan mulki a Najeriya, yana fatar ganin irin haka a wannan lokaci.

Sanat Ali Ndumi yana cikin wannan majalisa ta yakin nemarwa shugaban Muhammau Buhari zabe, yace shugaban kasa ya gargadesu da suka aiki bisa ka’ida kuma su bayyanawa jama’a irin nasarori da gwamnati ta samu da kuma irin sauyi na kwarai da aka samu a Najeriya ba tare da in zarafi ko tsangwamar wani ba.

Daga birnin tarayya Abuja, ga rahoton Umar Faruk Musa:

Your browser doesn’t support HTML5

BUHARI YA KADDAMAR DA KWAMITIN KEMPE