Tashar karbar kayayyakin da aka taho da su ta teku da shugaba Buhari ya kaddamar yau a birnin Kaduna ita ce ta farko cikin guda bakwai da gwamnatin tarayya za ta kafa.
Sauran tasoshin kan tudun za'a kaddamar dasu a garuruwan Ibadan, Aba, Kano, Jos, Funtua, da Maiduguri wadanda shugaban ya ce aiki na tafiya a kansu kuma ya yi nisa.
A cewar shugaban tashar sauke kayan teku a kan tudu da aka kaddamar a Kaduna za ta magance cunkoson da akan samu a tasoshin ruwan Najeriya da kan hanyoyin kasar. Haka ma za'a rage kudaden da ake kashewa ta hanyar sufuri da hada hadar kasuwanci a fadin kasar ta Najeriya.
Barrister Muhammad Hassan Bello shi ne shugaban hukumar hada hadar kasuwanci ta jiragen ruwa, ya yi karin haske game da ribar da Najeriya za ta samu akan tashar da aka kaddamar. Ya ce idan mutum ya sayo kaya daga kasashen waje ya na iya cewa su zo Kaduna ba tare da zuwa Lagos ba. Yin hakan ya sawaka kashe kudi da tsaikon da ake samu a tashar Legas. Daga Kaduna ana iya aika kaya kasashen waje. Wata hanya ce ta bunkasa tattalin arziki. Yanzu mutane wajen dubu uku zuwa dubu biyar ne zasu samu aiki a tashar.
Alhaji Aminu Bello daga jihar Sokoto da Alhaji Sani Gwamna daga jihar Zamfara suna cikin wadanda suka halarci bikin kaddamar da tashar. Sun ce sun samu wasika daga hukumar tashar jirage da ita gwamnatin tarayya cewa za'a kafa irin tashar Kadunan a garin Illela, garin dake kan iyaka da kasar Nijar.
Baicin kaddamar da tashar shugaban kasa ya kaddamar da taragu da kawunan jiragen kasa masu sauri da zasu dinga daukar fasinjoji daga Kaduna zuwa Abuja.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5