Shugaba Buhari da mataimakinsa Farfasa Yemi Osinbajo sun dukufa wajen yiwa kasafin kudin da majalisa ta maido masu binciken kwakwaf.
Duba kasafin kudin shafi shafi wani sauyin salo ne da ba'a saba gani a kasar ba. Shugaban na yanzu yana takatsantsan da lamarin kudi domin muradun yaki da zarmiya da aka saba yi can baya.
Kwamred Abubakar Abdulsalam dan rajin yaki da cin hanci da rashawa ya yadda da matakin da shugaba Buhari ya dauka na tabbatar cewa ba'a yi mashi coge ba. Yace hanzari bai taba haifar abu mai kyau ba. Yace a yi la'akari da lokacin da shugaban ya gabatar da kasafin kudin. Cikin kwanaki biyu aka ce kasafin ya bata. Daga baya kuma aka ce an samu wani.wanda aka ce yana kunshe da abubuwan da basa cikin na farko.
Abubakar Abdulsalam yace duk mutumin da yake da hankali dole ne ya zauna ya sake dubawa ko abun da ya mika aka mayar masa dashi. Idan an sa son zuciya ciki dole ne ya sa a gyara.
Mai taimakawa shugaban kan majalisar wakilai Kawu Simaila yace shugaban zai duba kasafin a tsanake saboda daukan matakin da ya dace. Yace ministoci ma suna dubawa kana su shaidawa shugaban abubuwan da suka gano.
Yanzu dai sai shugaban ya dawo daga ziyar zuwa kasar China za'a sanar da duniya yadda ta kwana.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5