A cikin sakon da ya aiko yayi godiya bisa ga duk addu'o'in da ake yi masa domin ya samu lafiya ya koma gida.
Shugaban ya bada tabbacin cewa babu hujjar nuna damuwa dangane da halin kiwon lafiyarsa saboda likitoci sun ce yana bukatar hutu ne domin ya kara murmurewa bisa ga bincike binciken da suka yi akan rashin lafiyarshi.
Malam Garba Shehu kakakin shugaban yayi karin haske bisa sakon na Shugaba Muhammad Buhari. Yace sako ne na godiya game da irin addu'o'in da ake yi masa. Shugaban ya ji ana yi masa addu'o'i a masallatai da coci-coci.
Yanzu dai ba za'a iya fada lokacin da zai dawo ba amma kakakin yace idan lokacin dawowarsa yayi za'a fada. Hutun na shugaba Buhari bai sabawa tsarin mulki ba domin yana da hutun kwanaki 45 bisa doka.
Farfasa Al-Mustapha Ujudud yayi karin haske akan matsayin doka. Yace tsarin mulki ya ba shuga ikon rubutawa shugabannin majalisun dattawa da na wakilai sanar dasu zashi hutu kana ya mikawa mataimakinsa mulki a matsayin mukaddashin shugaban kasa. Idan kuma har rashin lafiyan ba zai sa ya iya tashi ba sai an kafa kwamiti ya tabbatar. Amma bisa ga rashin lafiya kawai ba'a sa lokacin da zai dawo ba a dokance.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5