Shugaba Buhari Ya Gargadi Akantoci

Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya gargadi akantocin Najeriya da su goyi bayan gwamnatinsa wurin yakai da cin hanci da rashawa domin ta ci gajiyar arzikinta duk da faduwar farashen man fetur a duniya

Yau a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya shugaba Buhari ya umurci akantocin kasar su goyi bayan kokarin gwamnati da karfafa adalci da tabbatar da aikata gaskiya da yin mulki ba tare da wata rufa-rufa ba. Ya kara kira su mutunta dokokin yin anfani da kudade da kaddarorin kasa.

Yayinda yake jawabi da mambobin hukumar horas da akantoci da kula da harkokinsu wato ICAN a takaice a fadarsa ta Aso Rock Villa Shugaba Buhari ya jawo hankalinsu tare da yi masu gargadi akan faduwar farashen mai a kasuwar duniya duk da cewa man fetur ya zama hanya daya tilo da kasar ke samun kudaden shiga. Man fetur shi ne gimshikin tattalin arzikin kasar. Shugaban yace saboda haka dole kasar ta yi takatsantsan kan yadda take anfani da kudadenta idan ba haka ba kuma ta samu cikas wurin ayyukan cigaban kasa tare da maida ita baya.

Yace ku taimakemu mu koma lokacin da inda ba'a facaka da kudin kasa. Ko kwabo aka kashe an san dalilin yin hakan da kuma abun da aka saya dashi ko aka yi dashi.

Shugaba Buhari ya gargadi akantoci su maida hankali ainun akan kidigdigar kudaden da gwamnati ke kashewa domin a tabbatar da gaskiya. Wato idan sun zo duba takardun gwamnati kan yadda aka kashe kasafin kudin kasar kada su kuskura su yi rufa-rufa. Su bayyana komi a fili domin a tabbatar da cigaban kasar.

Ya sake jaddada hakan lokacin da ya juya kan shugaban akantocin Otunba Samuel Olufemi Deru domin ya tabbatar sun yi aikinsu tsakanisu da Allah.

Shugaban ICAN yayi maraba da dawowar yadda ake gudanar da aikin akanta da can, wato idan sun zo bincike su fede biri har bindi ba tare da gwamnati tana fada masu abun da suke son gani ba.

Yace rike gaskiya da adalci da shugabanci nagari su ne tushen sana'ar akanta. Saboda haka abun farin ciki ne a matsayinka na shugaban kasa ka rungumesu inji Deru.

Ya cigaba da cewa muna baka tabbacin goyon bayanmu dari bisa dari duka ilahirinmu saboda mu taimaka wurin gina kasa a tafarkin kulawa da kariya da rike al'adun dimokradiya da gina tattalin arziki mai dorewa saboda kasarmu ta zama zakarar kasashen Afirka.