Amincewa da fitar da kudi Naira miliyan 164 da shugaba Muhammad Buhari ya yi domin biyan kudin 'yan matan Chibok dake karatu a jami'ar ABTI dake Yola ya nuna yadda gwamnatin tarayya ke kulawa da matan da suka samu 'yanci tare da kwantar masu da hankali a makarantar da 'ya'yan masu hannu da shuni ne suke samun zuwa.
Kalilan daga cikin 'yan matan da suka samu 'yanci sun samu tafiya kasar Amurka karatu amma yanzu yawancinsu suna jami'ar ABTI wadda mallakar tsohon mataimakin shugaban Najeriya ne, Alhaji Atiku Abubakar.
Gwamnatin Najeriya ta hannun ministar mata Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta bayyana dalilan da suka sa ta tura duka 'yan matan jami'ar ABTI, mai zaman kanta. A cewarta ABTI ita ce kadai jami'a daya tilo da take da tsarin karatun da ya dace da 'yan matan domin su samu natsuwa su yi karatunsu. Ta kara da cewa mata 57 da suka tura wasu makarantu a Jos da Zaria sai da suka maida dukansu ABTI saboda makarantun sun ce basu da irin tsarin ABTI da zai taimakawa matan.
Yusuf Ishaq Baji wani dan jarida ya ce biyan Nera miliyan 164 da gwamnatin tarayya ta yi a madadin 'yan matan wa jami'ar ABTI tamkar ita gwamnatin bata da kwarin gwuiwa ne akan nata jam'o'in ne.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5