Bayan kalubalantar gwamnatin Buhari da tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya yi da cewa ta gaza, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce shugaba Muhammadu Buhari na da sauran damar gyara Najeriya.
Bafarawa ya yi furucin ne yayinda yake zantawa da manema labarai a Abuja inda ya ce bai gamsu da ikirarin gwamnatin Buhari ba na cewa ta samar da ingantacen tsaro. Ya yi misali da yawan satar mutane da labaran yadda Boko Haram kan kai hare-hare.
Bafarawa ya ce a matsayinsa na dan kasa ya na da damar ya ba shugabansa Buhari shawara amma kuma bin shawarar ya rage ga shugaban.
Duk da cewa gwamnati na ikirarin samun tsaro, Bafarawa ya ce maganar fatar baki ce kawai domin talakawan kasar basu gani a kasa ba. Ya ce yanzu mutane na tsoron shiga mota daga Kaduna zuwa Abuja, jirgi suke shiga saboda tsoron masu sace mutane.
Amma babban sakataren APC, jam’iyyar dake mulki, Alhaji Mai Mala Boni ya ce gwamnati ta yi duk abun da ya dace har da tsaro dake cikin samun nasara. Ya ce ba sa mamaki idan dan PDP ne ya fito yana sukar gwamnatin yanzu. Yace a lokacin gwamnatin PDP, Masallaci ko Coci ba’a isa a shiga ba saboda tabarbarewar tsaro. A lokacin gwamnatin PDP hatta kudaden sayen makamai sace su aka yi. Sakataren yace barnar da ‘yan PDP suka yi ne Shugaba Buhari yake gyarawa a yanzu.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5