Keften Yusuf Abdulmalik sakataren yada labarai na kungiyar tsoffin sojojin Najeriya reshen jihar Kano shi ya yiwa 'yan jarida jawabi inda ya bayyana korafinsu game da rashin biyansu kudaden fansho tun daga lokacin gwamnatin shugaba Jonathan.
Yace lokacin da Janar Buhari ke kemfen neman zabe ya yi masu alkawarin biyansu kudadensu. Yace sun yadda dashi saboda shi ma tsohon soja ne, wato daya daga cikinsu. Yace sun bashi a rubuce halin da suke ciki.
Batun makalewa ko badakalar kudaden fansho da hakokin ma'aikatan da suka yi ritaya a Najeriya ba sabon abu ba ne wala a matakin tarayya ko na jiha musamman idan an yi la'akari da rikice rikicen da suka shafi hakokin ma'aikata a kusan kowane lokaci.
Malam Mansur Datti malami a Kwalajin Fasaha ta Kano kuma kwararre kan lamuran kwadago da nagartar aiki ya yi tsokaci. Yace fansho nada alaka da duk wanda yake dan kasa ne ba sai wanda ya yi aikin albashi ba. Dan kasuwa yana bukatar lokacin da zai huta ya samu natsuwa shi ma a dinga biyansa kamar yadda ya rike tattalin arzikin kasa. Idan ma'aikaci ne akwai lokacin da yake son ya je ya huta saboda karfinsa ya kare tunanensa kuma ya soma samun rauni ga kuma iyali sun yi masa nauyi. To shi ma jama'ar da ya bautawa su ma su zo su rikeshi.
Malam Mansur yace amma yadda Najeriya take harkar fansho da biyan hakokin ma'aikata bayan sun bar aiki, hakika harka ce mai bata rai. Babban abun da zai tayarwa mutum rai shi ne yau a duba yadda tsarin 'yan fansho wadanda suka bar aikin soja yake. Sojan nan dake bakin aiki shi ne yake tauye hakinsu. Haka ma 'yansanda idan suka yi ritaya kwana bakwai ake basu su bar gidajensu su kuma cire 'ya'yansu daga makaranta.
Malam Mansu ya cigaba da cewa bincike ya nuna cewa ma'aikatan gwamnati da suka yi ritaya sun fi kowa kamuwa da cutar hawan jini da cutar sikari. Irin wadannan mutanen suna bukatar a taimaka masu amma a karshe sai a ga cewa biyansu fansho ya zama bala'i. Ma'aikacin da ya kamata ya taimakawa wadanda suka yi ritaya ganin cewa wata rana shi ma zai yi ritaya sai ya zama umalubaisan kawo mugun cikas wurin biyansu. Irinsa ne suke tauyewa 'yan fansho hakinsu.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5