A cigaba da ja-in-jar da ake yi tsakanin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Majalisar Dokokin kasar kan batun sabunta jadawalin zabe, bayan da Shugaba Buhari ya bayyana ma Majalisar dalilansa na kin sanya hannu kan kudurin dokar sauya jadawalin zaben, wasu ‘yan Majalisar sun mai da martani.
Tuni dai aka shiga muhawara kan wannan batu a fadin kasar. Kudurin dokar gyarar dokar zaben, ya nuna cewa za a soma zaben ne da na Majalisar Dokokin Tarayya kuma na Shugaban kasa ne zai zo karshe. Wannan ya saba ma yadda ya ke a yanzu, wato yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta tanadar a kundin zaben da ta bayyana a watan Nuwamban bara.
Sanata Shehu Sani dan jam’iyyar APC, ya ce yanzu ya rage ga Majalisar ta kada kuri’a tsakanin masu goyon bayan matsayin Shugaba Buhari da kuma masu ra’ayin Majalisar Dokokin kasar. Ya ce duk bangaren da ya yi rinjaye ra’ayinsa ne zai tabbata. Shi kuwa wani dan Majlisar wakilai mai suna Ahmed Babba Kaita ya ce matakin da Shugaba Buhari ya dauka ya yi daidai:
Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5