Shugaba Buhari Bai Taya Ni Murnan Cin Zabe Ba.

  • Ladan Ayawa

Women cast their votes during a local government election in Nigeria's commercial capital Lagos October 22, 2011. Lagos state Independent Electoral Commission registered 6.2 million voters who took part to elect leaders for 20 local government areas in Ni

Shugaba Buhari bai amsa ya zama cikakken dan demokaradiyya ba wajen rashin taya ni murnan lashe zabe.

Gwamna Sirieke Dickson na jihar Bayelsa ne ke wannan kalamin sailin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja kan nasarar lashe zabe karo na biyu a karkashin tutar jamiyyar PDP da yake samun sakon taya murna daga shugaba Buhari.

Yakamata da yayi koyi da yadda tsohon shugaba Jonathan ya taya shi murna tun gabanin sanar da sakamakon zabe.

Haka Gwamna Dickson yayi kira ga abokin takarar sa Timipreye Silva na jamiyyar APC da yazo su hada kai.

Yace naji yana cewa zaije koto amma kowa yasa na lashe wannan zaben.

Tsohon mataimakin kakakin kakakin majilisar wakilai Chibudo Nwuche wanda ada dan PDP ne amma yanzu ya koma APC yace ai aiki ake so na raya kasa ba maganar taya murna ba.

Nwuce yace zaka ga ko a bikin murnan haihuwa mutane na cika shafunan jaridu da taya manyan mutane murna da haka yayi hannun riga da muradun canji na gwamnatin Buhari.

Ga dai Nasir Adamu El-Hikaya da Karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Buhari Bai Taya Ni Murnan Cin Zabe Ba.2'43