ABUJA, NIGERIA - Shugaba Tinubu ya nada mataimakinsa Kashim Shatima a matsayin shugaban Majalisar da kuma wasu muhimman mambobin Majalisar da suka hada da gwamnonin jihohi 36, gwamnan babban bankin kasa, Ministan kudi, da sauran shugabannin hukumomin gwamnati da abin ya shafa.
Babban makasudin Majalisar ta (NEC) shi ne aiwatarwa da bayar da shawarwari masu ma'ana kan tsarin gwamnati na ci gaban tattalin arziki.
Shugaba Tinubu ya bayyana kudurinsa na gudanar da mulki ba tare da son rai ba, tare da tabbatar da cewa, gwamnatin tana gudanar da ayyukanta kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada da kuma bin doka da oda.
Wannan yunkuri na da nufin samar da gaskiya, rikon amana, da kuma yanke shawara mai inganci a cikin majalisar.
A yayin jawabin da ya yi wa Majalisar ta tattalin arzikin kasa, Shugaba Tinubu ya bayyana irin sadaukarwar da gwamnatin ke yi na inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.
Ya kuma jaddada muhimmancin gudanar da mulki da ke bin kundin tsarin mulki da bin doka da oda, tare da kare al'ummar kasar daga ta'addanci da ayyukan laifuka daban-daban.
Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatin na bunkasa tattalin arzikin kasa, samar da ayyukan yi, samar da abinci, kawar da fatara, da sanya mata da matasa a dukkan harkokin ci gaba.
Ya kuma jaddada abubuwa guda takwas da gwamnatin ta sa a gaba: da suka hada da tsaro, tattalin arziki, ayyukan yi, noma, da samar da ababen more rayuwa.
Shugaban kasar ya bayyana matakan da gwamnati ta riga ta dauka, kamar kawo karshen tallafin man fetur da kuma hada kan farashin canji. Tinubu ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da matakan kawo sauyi da nufin bunkasa tattalin arziki ba tare da haifar da hauhawar farashin kayayyaki ba.
Da yake bayyana kalubalen da ke gabansa, Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi 36 na Najeriya da kananan hukumomi da su hada karfi da karfe wajen bunkasa ababen more rayuwa cikin gaggawa.
Ya jaddada cewa hadin gwiwa na da matukar muhimmanci domin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci da kuma cimma muradun al’ummar Najeriya.
Tinubu ya bayyana godiyar sa ga mataimakinsa Kashim Shatima da daukacin ‘yan Majalisar, inda ya amince da kudurin su na yin gyara mai ma’ana da zai yi tasiri mai kyau ga rayuwar ‘yan Nijeriya.
Ya bayyana kwarin gwiwa kan yadda Majalisar za ta iya bayyana manufofi da shirye-shiryen da suka dace da jama’a da za su magance matsalolin da al’umma ke ciki.
Bayan nasarar kaddamar da Majalisar tattalin arziki ta (NEC) da Shugaba Ahmed Tinubu yayi, yanzu daukacin al’ummar kasa na cigaba da bibiya da sanya ido ga Majalisar wajen kawo shawarwarin ta zuwa ingantattun manufofin gwamnati.
Al'ummar Najeriya na sa ran aiwatar da gyare-gyaren da za su samar da ci gaba mai dorewa, ingantacciyar rayuwa, da ci gaban tattalin arziki.
(Yusuf Aminu Yusuf ya bada gudummuwa a rubuta labarin)
Saurari cikakken rahoton daga Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5