Shoprite ya bayyana wannan matakin ne a cikin wata wasikar da ya aikewa kungiyar kwadago ta kasar Kenya.
"Za mu rufe shagonmu na City Mall da ke garin Nyali a birnin Mombasa, kafin karshen wannan watan da müke ciki," in ji kantin.
Hakan dai na faruwa ne kasa da shekara daya bayan da aka bude shagon na Shoprite a Mombasa.
A ranar Litinin din da ta gabata Shoprite ya dauki wani mataki makamancin wannan a Najeriya inda ya bayyana yana nazarin rufe dukannin shagunansa da ke kasar Najeriya.
Lamarin da bai yi wa 'yan kasar dadi ba sakamakon yadda ake fargabar mutane za su rasa ayyukan yi sannan wuri ne da jama'a ke zuwa a lokutan bukukuwan sallah da na kirsimeti.
Shoprite ya alakanta wannan matakin da yake ta dauka da yanayin yadda kantunan nasa da ke kasashen waje suke kawo musu ci gaba ko koma baya.