Shirye-shiryen Sallar Azumi a Najeriya

Yan Kasuwa Na Auna Shinkafa

Yayin da ake shirye shiryen gudanar da sallar Idi a wasu sassan Najeriya, talakawa a kasar sunce sallar bata da armashi, saboda yanayin matsin rayuwa, sakamakon zaman gida da hukumomi suka tilasta musu saboda annobar cutar coronavirus.

Muryar Amurka ta zanta da ‘yan Najeriya masu yawa lamarin dake bayyana halin da talakawa a Najeriya za su gudanar da sallar bana saboda yanayin da annobar coronavirus ta jefa al’umma, wanda ya kara dagula lissafin rayuwar marasa karfi a kasar.

Sai dai a iya cewa, ba duka aka zama daya ba, domin kuwa wasu magidantan sun bayyana cewa sun shirya tsaf, domin tunkarar sallah.

Halin matsin rayuwa da galibin talakawa suka samu kansu a Najeriya, ya sanya su-ma ‘yan kasuwa na kokawa saboda yanayin rashin ciniki. Kamar yadda Malam A. Zango guda cikin masu sayar da kayan miya ya ce bana kam babu kasuwa kamar yadda aka saba a baya.

To ko me talaka musulmi ya kamata ya yi a cikin irin wannan yanayi? Malam Mustafa Muhammad Dandume, ya ce abin da talaka ya kamata ya yi shine hakuri, domin halin da Allah ya saka talaka wani matsayine na daban.

Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Shirye-shiryen Sallar Azumi a Najeriya - 3'17"