Shirye-shiryen Rantsar Da Sabon Shugaban Amurka

Zababben shugaban Amurka Donald Trump da matarsa Melania

Ana shirin bukin rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka na 45.

A yau juma’a da missalin karfe shida na yamma agogon Najeriya ake sa ran rantsar da shahararran mai kudinnan kuma ‘dan kasuwa Donald J. Trump, a matsayin shugaban Amurka na 45.

A jiya ne Donald Trump ya yi hasashen cewa da zarar an rantsar da shi “Amurka za ta ga wani abin al’ajabi.”

Trump yayi alkawarin yin aiki tukuru wajen ganin ya hada kan kasarsa, ya kuma dawo da martabar Amurka ga Amurkawa.

Bayan kammala bukin rawa da aka yi a yammacin jiya Alhamis a dandalin Lincoln Memorial, Trump yace bai damu ba idan yanayi zai yi kyau ko a’a a yau juma’a, yana mai gayawa duniya dake kallon abin da ke faruwa a Amurka.

Anyi hasashen cewa a yau lokacin bukin rantsarwa akwai yiwuwar samun sanyi da kuma ruwan sama.