Shirye Shirye Sun Kamala a Zaben Gwamnan Jihar Bayelsa

INEC

Kawo yanzu dai shirye shirye sun kamala a zaben Gwamna da za’a gudanar a jihar Bayelsa, kimani jami’an tsaro dubu goma sha hudu ne aka jibge domin tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan Sanda sojan sama da jami’an SSS.

Dukkanin jami’an tsaron daga wajen jihar aka dauko su domin tabbatar da tsaro a wannan zabe da za’a gudanar gobe Asabar.

Jihar Bayelsa dai tayi kaurin suna wajen tabarbarewar tsaro da kuma tashe tashen hankula masasmman na siyasa, inda bayanai suka nuna kawowa wannan gabar an kasha mutane da dama a jihar sakamakon hare hare ko a jiya ma dai sai da aka bayana kashe wani shugaban karamar hukuma.

Rundunar ‘yan Sandan jihar ta Bayelsa ta tattauna da shuwagabanin jam’iyu domin kaiwa ga zaman lafiya a zaben na gobe Asabar, rundunar ‘yan Sandan Najeriya, ta ce ta shiryawa zaben D.I.G mataimakin sufeto janar na ‘yan Sanda Najeriya, Hashimu Salihu Arugungu, shine wanda aka turo jihar ta Bayelsa domin jagorantar tsaro a jihar.

Itama hukumar zabe mai zaman kanta a jihar ta bayyana cewa tuni ta shiryawa zaben inda ta rarraba kayan aiki a sassa daban daban na jihar, sai dai kuma bayanai na nuni da cewa a wasu sassan jihar akwai wasu kayayyakin aiki da basu isa ida yakamata ace sun kai ba , hukumar zaben ta ce lallai komai zai tafi yadda yakamata, kmimani jam’iyu 20, ne zasu fafata a zaben na Gwamna.

Your browser doesn’t support HTML5

shirye shirye sun kamala a zaben jihar bayelsa - 3'35"