Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya ce, duk da wasu ‘yan tashe-tashen hankula da aka fusakanta, shirin tsagaita wutar da aka cimma ya shiga yini na uku.
WASHINGTON DC —
Mr Ban ya kara da cewa yanzu haka wata runduna ta musamman na sa ido a shirin tsagaita wutar, domin kada a samu bazuwar tashin hankali da aka samu a wasu wurare.
Ministan harkokkin wajen Faransa Jean- Marc Ayrault, ya kira wani taron gaggawa, domin tattaunawa kan yankunan ‘yan tawaye da aka ce an kai ma hare-hare.
A ranar Asabar din da ta gabata, shirin tsagaita wutar ya fara aiki, inda aka samu korafe-korafen cewa duk bangarorin da suka amince sun keta dokar shirin na tsagaita wuta.
Su dai bangaren ‘yan adawa sun yi korafin cewa dakarun Bashar al Assad sun kai hare-hare a wasu garuruwa da ke hannunsu.