Yayin da wasu Fulanin da ke jahohin kudancin Najeriya ke marhaban da shirin rajistar Fulani makiyaya a yankin, wasu na watsi da shirin da cewa tunda su ‘yan Najeriya ne bai kamata a yi masu rajista ba. Shugaban kungiyar Miyatti Allah na jahar Ondo, Alhaji Garba Bello ya ce babu wata matsala game da batun rajistar tunda dama can kungiyar Fulani ta Miyatti-Allan ta na da rajista. Ya ce dama an sa Shugabannin kungiyar Miyatti-Allah ta kasa su yi rajistar Fulani a dukkannin jahohin Najeriya. Y ace dukkan Fulanin jahar Ondo an masu rajistar.
Alhaji Bello ya yi kira ga duk wani Bafulatanin da bai yi rajista ba da ya yi. Y ace ko ba komai ya kamata a ce kowani Bafulatani ya yi rajista a duk jahar da ya ke. Da aka tambaye shi ra’ayinsa idan gwamnatin jahar Ondo ta ce da ita za a yi rajistar sai y ace tunda hukuma ce, idan ta bukaci hakan za su tuntubi shugabanninsu su ga ko ya dace da dokar kasa, idan ya dace sai su yi. Y ace ya kamata duk mai son zaman lafiya ya bi umurni muddun bai saba da dokar kasa ba.
Shi kuwa Shugaban Miyatti-Allah na jahar Oyo watsi ya yi da batun shirin rajistar. Ya ce wamman zancen bai “shige su ba.” Ya ce batun a yi ma Fulani rajista a jahar Oyo ba zai yiwu ba saboda su ba ‘yan kasashen waje ba ne, su ‘yan Najeiya ne. Ya ce idan gwamnati ta ce dole su yi rajistar za su zauna da ita su nuna ma ta rashin dacewar rajistar saboda bai dace ba a yi ma wasu ‘yan Najeriya rajista ta daban. Ya ce muddun aka masu rajista to sun zama ‘yan kasar waje Kenan. Ya ce sam babu wasu ‘yan kasashen waje da su ka saje da su don haka duk Fulanin da ke jahar Oyo ‘yan Najeriya ne. Ya ce su Fulanin yankin kudu maso yammacin Najeriya ba su amince da rajistar ba.
Ga Hassan Umar Tambuwal da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5