An bayyana yin garambawul, ga shirin gwamnatin tarayyar Najeriya, na “N POWER” a matsayin matakin farko na sa shirin kan kyakkawar turba, domin cimma burin Gwamnati akan shirin.
Wani matashi Umar Muhammad Gombe, ne ya furta haka a zauren matasa a shirin muryar Amurka, nay au da gobe, inda yake cewa na biyu kuma shine a wayar da jama’a kai akan shirin kamar yadda ya kamata.
Ya kara da cewa yakamata a tabbatar da cewa akwai tsarin raba dai dai ta yadda kowace karamar hukuma zata san anayi da ita, a fadin Najeriya.
Shi kuwa al-Amin Ciroma, cewa yayi akwai wata babbar matsala inda har yanzu akwai matasa masu karatu da kuma karfi a jika amma babu aikin yi sai zaman karkashin bishiya, irin wandannan su yakamata abi su unguwa unguwa, da taimakon masu unguwani da dakattai.
Ya kuma kara da cewa sau tari akwai abubuwan da yake fargaban bugawa a jarida saboda da zarar ka buka a jarida sai kaji ana cewa ka zagi Buhari, yana mai cewa “shin idan shi shugaba Buhari ba nawa bane idan yana abu bazan damu ba amma saboda na yarda da aiyukan da yake yi idan yayi abinda ba dai dai ba dole in fito in fada masa domin ba zai taba zama koina yana nan ba”.
Ya ci gaba da cewa Gwamnatin da kake kishi ita ka kewa nuni da kurakranta domin ta gyara akwai kyawawan, manufofi tattare da shugaba Muhammadu Buhari, amma wajen aiwatar dasu shine yakamata Gwamnati tasa abubuwa yadda yakamata su kasance.
Your browser doesn’t support HTML5