A baya ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun karbe ikon garuruwa da dama kafin daga baya dakarun Najeriya su kwato ikon garuruwan.
Gabanin hakan, hukumomi a matakai daban daban, sun kafa sansanonin ‘yan gudun hijra a sassan yankin domin a baiwa ‘yan gudun hijrar mafaka.
Rahotanni na nuni da cewa kangin da wasu garuruwa suka shiga a yankin, ya sa yara kanana da dama cikin mawuyacin halin matsalar karancin abinci mai gina jiki, da kuma isasshen abincin a daya bangaren.
A ‘yan kwanakin nan hukumar da ke tallafawa kananan yara ta Majalisar Dinkin duniya ta yi kiyasin cewa akalla kananan yara dubu 50 ne za su rasa rayukansu idan ba a dauki kwararan matakai ba saboda yunwa da karancin abinci mai gina jiki.
Majalisar Dinkin Duniya ta kara da cewa akwai kuma yuwuwar sama da yara dubu 250 su yi fama da matsalan karancin abinci a wannan shekara.
To sai dai a wannan mako ne gwamnatin Najeriya ta shata wasu matakai da za ta bi domin ganin a shawo kan wannan matsala.
Domin jin wadannan matakai da tsare-tsare, saurari rahoton da waklin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina ya aiko daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5