Shirin Kare Jama'ar Borno daga Ambaliyar Ruwa

Gwamnan jihar Borno Ibrahim Kashim Shettima

Yayinda hukumar harsashe yanayi ta fitar da rahoto ceewa wasu jihohin Najeriya zasu yi fama da ambaliyar ruwa, jihar Borno dake cikin wadannan jihohi tana daukan wasu matakan kare al'ummarta da dukiyoyinsu

Sakamakon ruwan sama mai karfi da za'a samu cikin watannin Agusta zuwa Oktoba na wannan shekara hukumar tace za'a samu ambaliyar ruwa a jihohin Kaduna, Kwara, Nasarawa, Yobe, Zamfara, Akwa Ibom, Bauchi, Borno, Cross River da Delta.

An dade ana samun ambaliyar ruwa a wadan nan jihohi musamman a garuruwan dake bakin kogi inda sau tari a kan bukaci jama'a da su gujewa gine-gine a bakin kogi domin gudun abun da ka kai ya komo.

Toshe magudanar ruka kan haddasa ambaliyar ruwa lamarin da kan asa ruwan tumbatsa ya kuma kwarara zuwa cikin gidajen mutane.

Hukumar kula da muhalli ta jihar Borno tace tana iyakar kokarinta na ganin jama'ar jihar bas fada cikin wannan bala'in ba.Tace kullu yaumin suna yashe magudanar ruwa tare da hana mutane toshesu domin kaujewar ambaliyar.

Alhaji Ali Sirimi shugaban hukumar ta jihar yayi karin haske dangane da shirin da su keyi. Yace suna bude duk magudanan ruwan da ya yi kogi saidai babbar matsalarsu ita ce ta mutane dake ruba bola a magudanun. Haka kuma rikicin Boko Haram ya hanasu yashe kogunan kansu abun da a da suna yi kowace shekara.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Shirin Kare Jama'ar Borno daga Ambaliyar Ruwa - 3' 50"