Shirin Gwamnatin Buhari Na Samarwa Da Matasa Aiki Na Fuskantar Matsala

Shugaba Buhari da Mataimakinsa Farfasa Osinbajo wanda shirin matasan ke karkashinsa

Shirin da gwamnatin Buhari ta gudanar na samar ma matasa ayyukan yi domin inganta rayuwarsu ya shiga wata matsala inda matasa a jihohi takwas ke korafin rashin samun ko kwandala a matsayin albashi daga gwamnatin.

Muryar Amurka ta zanta da wasu daga jihohi takwas da lamarin ya shafa domin jin ta bakinsu kana ta tunkari jami'in dake kula da shirin don samun bangaren gwamnatin Buhari.

Wani malam Musa daya daga cikin matasan da suka ci gajiyar wannan shirin yace tunda ya soma aikin bai samu albashi ba wajen watanni hudu ke nan. Ya tabbatar cewa tunda suka fara ba'a biyasu ko sisinkwabo ba. Acewarsa duk wani bayani da ake nema sun bayar.

Wata malama ma bayan ta godewa gwamnati da kirkiro da shirin tace ba'a biyasu ba. Duk da korafe korafen da suka yi wai har yanzu ba'a biyasu ba.

To saidai wakilin gwamnati yace ba duka ba ne suka samu matsala. Yace matsalar da aka samu ta samo asali ne daga banbancin sunayensu da basu zo daidai da sunayen dake kan katunan shaida da suke rike dasu ba.

A cewarsa wasunsu suna komawa daga baya su canza sunayen da suka yi anfani dasu tun farko. Wasu kuma sun nemi canza bankuna. Yayi misali da jihar Kano inda suka fi samun koke koke mafi yawa.

Jami'in ya dora laifin ne akan matasan amma ya sha alwashin nan da dan karamin lokaci zasu warware matsalar su ma su soma samun albashinsu.

Jihohin da suka samu matsala sun hada da Borno, Jigawa, Kano, Katsina, Edo, Ondo, Imo, da Oyo.

Ga tattaunawar da Jummai Ali tayi.

Your browser doesn’t support HTML5

Shirin Gwamnatin Buhari Na Samar Ma Matasa Aiki Na Fuskantar Matsala - 3' 47"