Idan rahotannin da ke fitowa daga Janhuriyar Nijar su ka tabbata to shakka babu kasar ta fara shiga wani sabon babi na rigimar siyasa.
WASHINGTON, D.C. —
Da alamar dai siyasa Janhuriyar Nijar na kara shiga wani yanayi na rashin tabbas, saboda rahotannin da ke nuna cewa hukumonin kasar sun fara daukar matakan murkushe ‘yan adawa.
Ko a yau dinnan ma, yayinda ake kyautata zaton da yammacin yau Asabar tsohon kakakin Majalisar Dokokin Janhuriyar Nijar HAMMA AHMADU zai dawo birnin Yamai bayan da ya shafe fiye da shekara guda ya na gudun hijira a kasar Faransa sakamakon zarginsa da safarar jarirai daga Najeriya, rahotanni na nuna cewa hukumomi sun cafke wasu kusoshin jam’iyarsa ta MODEN LUMANA.
Ga wakilinmu Sule Mumuni Barma da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5