Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin ƙaddamar da shirin ɗaukar mutane marasa aikin yi dubu 774,000 aiki a faɗin ƙasar, wanda aka fara a jiya Talata, 5 ga watan Janairu na wanan shekara da muke ciki..
Ministan kasa a Ma'aikatar Ƙwadago, Festus Keyamo ne ya sanar da haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter. A sanarwar da Keyamo ya wallafa, ya ƙara da cewa dukkan ofisoshin hukumar ɗaukar aiki na (NDE) na jihohi ne suka fara shirin, kamar yadda aka tsara. Kuma tuni har an fara daukar matasan daga jiya Talata.
To saidai wannan yunkuri ya dauki hankali ganin cewa makonni biyu da suka wuce Majalisar Wakilai ta yi kudurin dakatar da wannan shirin na daukar marasa aikin yi a bisa dalilin cewa akwai wata manakisa da aka shirya wajen tantance wadanda za a dauka aikin.
To saidai ga Shugaba Kwamitin Kwadago da Daukar Ma'aikata a Majalisar Wakilai, Injiniya Mohammed Ali Wudil, ba a yi wannan kaddamarwar da amincewarsu ba, saboda akwai Kuduri da Majalisar Wakilai ta riga ta gabatar wanda a ciki an hana Ma'aikatar Kudi bada kudin yin wannan aiki har sai an tuntu6i Majalisar.
Injiniya Wudil ya ce bangaren Gwamnati ya yi gaban kansa ne ba tare da amincewar Majalisa ba. Amma mai ba shugaba Buhari shawara a harkar matasa, Nasiru Adahama, ya yi karin haske cewa Gwamnati ta tsara ɗaukar mutane 1,000 daga kowace karamar hukuma daga cikin ƙananan hukumomi 774 na ƙasan nan baki daya domin rage yawan matasa marasa aikin yi ne.
Adahama ya ce wannan shiri zai yi tasiri saboda an bi ka'ida wajen tantance wadanda za a dauka aiki kuma zai ba wadanda suka ci gajiyar aikin damar dogaro da kansu nan gaba.
Amma kuma wasu matasa irinsu Abdullahi Sabo daga Karamar hukumar Kuje sun yi sambarka da ganin wannan rana, inda ya ce a halin da ake ciki yanzu idan ka ba matashi wanda bashi da ko sisi dubu ashirin a lokaci daya, ka taimake shi sosai.
Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya tsakani Majalisar Wakilai da bangaren gwamnati a daidai lokacin da Majalisar za ta dawo bakin aiki a ranar 26 ga wanan wata.
Ga Madina Dauda da cikakken rahoton ta sauti:
Your browser doesn’t support HTML5