Wani bincike ya nuna cewa kimanin matasa 500 ‘yan kasar Kenya ne suka shiga cikin kungiyar ta Alshabab, wanda sakamakon haka gwamnatin kasar Kenya ta fito da tsarin yin afuwa ga matasan da suka shiga kungiyar matukar zasu ajiye makamansu.
Ministan harkokin cikin gidan Kenya ya tabbatar da haka tare da cewa suna son canza wannan lamari ta hanyar basu ayyukan yi da kuma daukar nauyin wasu su koma makarantu don su manta da canza musu tunani da kungiyoyi irin su Al-Shabab ke yiwa matasa.
Hare-haren baya-bayan nan na kungiyar sun sha fadar cewa suna kai shi ne a zuwa irin su Kenya don tursasawa kasar ta Kenya janye sojojinta da na kawance da suke yakarsu a Somalia. Cikin harin da aka kai a kenya har da na wani babban shagon saye da sayarwa da kuma na jami’ar Garissa a kwanan nan.
Wani mai fashin bakin al’amura Dakta Bawa Abdullahi Wase ya bayyanawa Muryar Amurka a hirarsa da Mahmud Lalo irin fahimtarsa game da lamarin na Kenya inda yace lallai hakan zai kawo mafita game da harkar tsaro a kasar.
Sannan yace in har kasa kamar Amurka zata janye sojojijinta a irin yadda ta taba yi a Somalia din duk da karfi tattalin arzikinta da karfi yakinta, me zai hana itama Kenya din ta yi hakan.
Wannan dai ba shine na farko da Kenya ta taba afuwa ga matasa ba, ta taba yi a shekarar 2012. Game da maganar gina shinge ko katangar da zata hana kwararar ‘yan ta’adda tsakaninta da wasu kan iyakokinta.
Dakta Bawa cewa yayi ai tunda katangar Barlin da aka taba yi a Turai bata yi aikin da ake so ba to ta Kenya ma in aka yi ba zata yi tasiri ba. Ya fi ganin dacewar magance matsalar ta hanyar tuntubar juna da sulhuntawa.
Your browser doesn’t support HTML5