Rahotanni daga fadar shugaban kasar Najeriya sun bayyana cewa 'yan majalisun tarayya sun lashe nera miliyan dubu goma sha uku cikin watanni biyu kawai bayan da aka rantsar dasu.
Kowane sanata ya samu alawus na fiye da nera miliyan 36 yayinda wakilai kuwa suka amshi fiye da nera miliyan 24.
To amma tsohon shugaban matasan APC wanda yanzu yana majalisar wakilai wanda kuma kafin ya shiga majalisar ya sha sukar albashin da suke karba, ya sauya ra'ayinsa.
Lado Suleja tsohon shugaban matasan APC yanzu ya daina kushe alawus din. Yae da ya shigo ya ga abun ba haka ba ne. Wai bita da kulli n ake yi. Idan an yi dalla dalla da kudin 'yan majalisun aka kwatantasu da wadanda suke waje banbancin bashi da yawa.
Rashin sanin abun da ke ciki musamman wai 'yan jarida su ne suke sa mutane na sukan albashin 'yan majalisun.
Akan wai wasu 'yan majalisun suna hawan motoci da kudinsu ya kai nera miliyan dari Lado yace akwai 'yan majalisu dake hawan motoci masu tsada kafin su shiga majalisar.
Tsohuwar minista a ma'aikatar ilimi da yanzu take majalisa Aishatu Jibril Dukku tana ganin ba tara dukiya ba ne a aikin majalisa fiye da kula da bukatun al'umma..
Saidai shugabannin addini na ganin cewa adalci ne kawai zai sa kowa more dimokradiya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5