Wani lauya Yakubu Sale Bawa yace ofishin matar shugaban kasa ko gwamnan jiha baya cikin tsarin mulkin kasa.
Masu sharhi sun ce galibi ana anfani da ofishin wajen bannatar da dukiyoyin jama'a wala a gwamnatin tarayya ko na jihohi. Lamarin ma har ya kaiga kananan hukumomi.
Akan wannan maganar mai magana da yawun fadar gwamnatin Najeriya Malam Garba Shehu ya bayyana matsayin shugaba Muhammad Buhari.Shugaban bai amince da ofishin "First Lady" ba. Ba ma sunan ba duk wani abun da doka bata yadda dashi ba ba zai karba ba.
Tunda babu shi a tsarin mulki shugaban kasa yayi alkawari ba za'a gudanar dashi ba.
Can baya akan ga matar shugaban kasa ko gwamna cikin tirkatirkan motoci da jerin gwano da jiniya. Ban da haka har ma ana nada masu ma'aikata wadanda da ake biyansu da kudin talakawa.
Kundun tsarin mulkin Najeriya ya tanadi ofishin shugaban kasa da na mataimakinsa sai kuma na gwamna shi ma da mataimakinsa.
To saidai wata tsohuwar 'yar majalisar tarayya ta goyi bayan ofishin tana cewa idan an haramta wato an cire mata daga harakar gwamnati ke nan domin babu wanda zai kula dasu.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina
Your browser doesn’t support HTML5