Bisa ga alamu da wasu labarai wadan nan mutanen ukku da yanzu ake nemansu sanannu ne ga sojojin Najeriya saboda haka bayyanasu a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo ya kawo daurin kai.
Muryar Amurka ta zanta da Kanar Sani Kukasheka kakakin rundunar sojin Najeriya ya bayyana wa duniya dalilin da yanzu suke neman mutanen ukku.
Kanar Kukasheka yace suna zaton mutanen ukku suna da alaka da kungiyar Boko Haram, kungiyar da ta kasance ta 'yan ta'ada, kuma ta aikata ta'adanci matuka a kasar. Suna kuma zaton bayanan da suke nema wadannan mutanen ukku suna dasu.
Yace sanin kowa ne 'yan ta'adan sun kashe mutane da dama. Sun hallaka dukiyoyin jama'a. Sun sace mutane ba iyaka musamman 'yan matan da suka sace daga makarantar sakandare ta 'yan mata dake garin Chibok cikin jihar Borno.
Sojoji sun dade suna ta cigiyar 'yan matan tare da rokon mutane su bada taimako ta hanyar bada bayanai da ka iya kaiga gano 'yan matan.
Kanar Kukasheka yace fayafayan bidiyo biyu da 'yan Boko Haram suka fitar kwana kwanan nan sun nuna akwai alaka tsakanin kungiyar da mutanen ukku. Akwai doka da ta tanadi cewa idan akwai yunkurin yin wani abu mara kyau wanda yake da labarin ya kamata ya sanarwa mahukumta. Amma su wadannan mutanen basu yi haka ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5