Hukumomin Nijar na ganin harin wani yunkurin kungiyar mujawo ne da nufin fitar da shugabanninta dake tsare a kurkuku.
To amma 'yan kasar Nijar na ganin matakin cigaba da ajiye 'yan ta'ada a gidan kaso a matsayin wata raguwar dabara.
Bayan Faransa da Amurka sun girke dakarunsu a Nijar domin yaki da ta'adanci sai gashi a baya bayan nan Jamus ta sanar da kafa sansanin sojojinta a kasar da nufin taimakawa dakarunta dake Mali.
Malam Mamman Sani Adamu wani mai sharhi akan al'amuran tsaro yana ganin kasancewar dakarun kasashen Turai a kasar na iya zama musabbabin hare-haren da Nijar ta fuskanta a jihohin Tawa da Taliberri. Inji shi tun shekarar 2001 Boko Haram take. Me ya sa sai daga shekarar 2012 kasar ta fara samun matsala da 'yan Boko Haram. Sai lokacin da wata gwamnati ta zo ta dorawa kanta biyan bukatun kasashen Turai shi ne 'yan ta'ada suka soma tada kayar baya.
Malam Mamman yayi misali da kasar Mali inda yace kasar Nijar ce ta fi kowace kasa kan gaba wurin shiga matsalar da Mali din ke fuskanta. Yace wannan tamkar karambani ne kawai. Inji shi, Nijar tayi hakan ne domin biyan bukatun turawa domin su taimaki gwamnatin ta dawama akan karagar mulki.
To saidai masu sharhi akan alamuran tsaro na zargin gwamnatin kasar da rashin ba sojojinta isassu da kuma ingantattun kayan aiki, musamman irin na zamani.
Shugaban kasar Nijar din Mahammadou Issoufou ya musanta zargin inda yace kashi goma cikin dari na kasafin kudin kasar ake anfani dashi akan ayyukan tsaro. Bugu da kari cikin shekaru biyar sau goma sha biyar gwamnati ta ninka kudin da ake ba fannin tsaro, inji shugaban kasar.
Wasu 'yan kasar sun ce son rai da son kai suka hana al'ummar kasar su gani a kasa.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5