Wasu iyaye da Median Dauda ta tattauna dasu a wata muhawara sun bayyana dalilan da suke gani su ne suka haddasa lalata tarbiyan 'ya'ya mata.
Idan an ce mata nada kwadayi wasu mazan ma basu kula da abun dake faruwa da 'ya'yansu ba. Ba sa yi masu tanadin da yakamata. Idan maigida ya fita daga gida bai bar wa matarsa abub da zata kula da gidan ba kuma wahala ta yi mata yawa dole ne ta bar 'ya'yan su lura da kansu.
Wasu mazan sun san matansu basu da sana'a amma si su fit asu barsu cikin mawuyacin hali har su shiga yin kwadayi. Idan maigida ya tanadarwa iylansa yadda ya kamata da kyar su dubi waje. Idan namuji ya tashi tsayi ya rungumi nauyin da Allah ya dora masa babu yadda za'a yi tarbiyar yara ta lalace.
Rashin imani ke sa wasu mazan su kare nasu 'ya'yan amma su lalata na wasu. To saidai kuma maganar tsiraici tana kara taimakawa wurin lalata yara mata.Akwai mazan da abincin da matansu suka girka bashi zasu ci ba. Sai su fita waje su ci abinci da aikata lalata.
Akwai wasu matan ma kome aka bata kanta ta sani. Akwai wasu mazan kuma a bigi nan a bugi can suke yi.
Akwai wasu matan da namuji zai bata kudi ta tanadawa 'ya'yanta duk abun da suke so amma ta ki kashe kudin.
Tarbiya nada tasiri akan rayuwar dan Adam. Duk mutumin da ya samu tarbiyar kwarai ba zai fita waje ya yi zina ba. Mace dake ta tarbiya mai kyau ba zata yi zina ba wai domin ba'a bar mata kudin cefane ba.
Akwai iyaye mata da basu damu da abun da 'yarsu ta kawo gida ba. Gani suke hakan birgewa ne, wato diyarta nada tagomashi a waje amma kuma bata san ko menene diyarta ke yi a waje ba. Duk wannan ya hadu da tarbiya.
Idan aka yiwa 'ya'ya tarbiya mai kyau ko makaranta suka je suka hadu da yara shashashu ba zasu bisu ba, zasu rike tarbiyar da aka yi masu a gida. A tarbiyar da yara a basu ilimi na addini to koina suka je ba zasu lalace ba.
Ga cikakkiyar muhawarar.