Shin Me Ya Sa Har Yanzu Farashin Kaya Bai Sauka Ba a Najeriya

Wai bangaren kasuwar Garki dake Abuja

'Yan Najeriya na mamakin yadda aka yi har yanzu farashin kayan abinci da wasu kayan bai sauko ba duk da cewa dalar Amurka ta yawaita domin 'yan kasuwa sun labe da karancinta da tsadarta ne.

Usman Sani yace har yanzu farashin kaya basu daidaita ba amma akwai sassauci a wasu kayan saboda buhun shinkafa ya kai Naira dubu ishirin amma yanzu ana samunsa Naira dubu goma sha takwas.

Malam Yushau Aliyu ya bayyana dalilin da ya sa farashin kaya bai sauko ba har yanzu. Yace farashin dala ya ta'allaka ne akan bukatun masu sayen kudin. Sai yawan kudin da bukatun 'yan kasuwa sun zo daidai farashin zai tsaya ta yadda zai shafi farashin kaya.

Alhaji Isa Sakatare wani shugaban 'yan kasuwa yace kayan da suka sawo da tsada can baya ba zasu sayar dashi da araha ba sai ya kare har sun sawo wasu kayan da araha sannan su daidaita farashi. Abu na biyu kasuwar bata tafiya dalili ke nan da ya sa kayan da suka sawo tun da dadewa suna nan a jibge. Farashin kaya ba zai sauka nan take ba sai idan farashin dala ya tsaya cik bai sake hawa ba na wani lokaci mai tsawo.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shin Me Ya Sa Har Yanzu Farashin Kaya Bai Sauka Ba a Najeriya - 2' 55"