Shin Me Ake Ciki Game Da Barayin Biro A Najeriya?

Biyo bayan jimillar kudin da gwamnatin Najeriya tace ta kwato daga barayin biro da kudin ke lissafe a Naira da Dalar Amurka da Fam din Ingila da Yiro na Turai, ba ayi karin bayanin shin maganar ta kare kenan ko za a ci gaba da jiran shari’a da yanke hukunci.

Duk da yake ba a ambaci sunayen mutanen ba don abinda fadar shugaban kasa tace bin ka’idar shari’a ko kuwa shawarar boye sunayen daga masana shari’a.

Madugun wadanda akafi sani an bankado kudade dayawa ta hanyar ofishinsa Kanal Sambo Dasuki, har yanzu yana hannun jami’an tsaro. Haka nan shima tsohon babban hafsan rundunonin sojan Najeriya Alex Badeh, wanda tabbas an buga hatimin hukumar EFCC a wani gidansa dake Abuja, dake nuna kwace gidan ko gidajen.

Sai dai rahotan da gwamnatin ta fitar yana nuna sharar fage ne kafin ci gaba da jiran dawo da jiran dawo da wasu kudaden daga ketare. Ko menene dokar da Najeriya ta tanada kan irin wannan yanayin? Ma’ana magana ta kare ne ko kuwa za a iya ci gaba da shari’a.

Lauya mai zaman kansa a Abuja Imran Adam, yace idan aka duba sashe na 175 sashe na 1, dokar tace shugaban kasa na da dama kan duk wani mutum da aka kama da laifi cewar zai iya sakinsa.

Yanzu dai za a jira aga yadda shari’a zata kaya ga wadanda ke a hannu yanzu kuma an kwato sauran kudaden, amma ba shakka akwai wadanda suka dawo da wasu kadaden asirce wanda kuma yanzu suke zaune a gidajensu.

Your browser doesn’t support HTML5

Shin Me Ake Ciki Game Da Barayin Biro A Najeriya? - 2'59"