Kungiyar ‘yan ta’adda ta IS ta tabbatar da mutuwar shugabanta Abu Bakr al-Baghdadi, kwanaki bayan da Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa an kashe shugaban 'yan ta'addan yayin wani samamen da sojojin Amurka suka kai a Syria.
Kamfanin dillancin labaran kungiyar na Amaq ya ce, Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurashi shi ne wanda aka nada a matsayin sabon shugaban kungiyar ta IS.
Haka nan an tabbatar da mutuwar mai magana da yawun kungiyar, Abu Hassan al-Muhajir, wanda jami'an Amurka suka ce an kashe a wani samame a Jarablus, a kusa da kan iyakar Siriya da Turkiyya, wanda aka gudanar kwana guda bayan wanda aka kai akan Baghdadi.
Jami'an sojan Amurka sun ce harin da aka kai wa Baghdadi, an kwashe watanni ana shirya shi, tare da tattara bayanan sirri daga mutane, a karshe, aka samu damar da ta dace don gudanar da samamen.