Shin Ko Ghana Za Ta Iya Cimma Yarjejeniya Da IMF Kafin Ta Gabatar Da Kasafin Kudin 2023?

Ken-Ofori-Atta da tawagar IMF

Ministan kudi na kasar Ghana Ken Ofori-Atta na da yakinin kulla yarjejeniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) kafin karshen shekara domin tallafa wa kasafin kudin shekarar 2023, sai dai masana na ganin tattaunawar za ta dauki tsawon kimanin wata shida.

Tun a watan Yuli ne dai aka fara tattaunawa tsakanin jami'an Ghana da na Asusun Lamuni na Duniya (IMF), daga nan ma’aikatar kudi da Bankin Ghana suka fara tattunawa da Asusun karo na biyu a ranar Litinin 26 ga watan Satumba na 2022, a wani yunkuri na ceto kasar da ke fuskantar matsalar tattalin arziki.

A cikin watan Nuwamba ne ministan kudi Ken Ofori-Attah zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 a gaban majalisar dokokin Ghana.

Ministan yace gwamnati za ta gaggauta yin shawarwari da Asusun don tabbatar da cewa muhimman shirye-shiryen gwamnati sun bayyana a kasafin kudin shekarar. Ofori-Attah ya fadi haka ne a wani taron manema labarai da ma’aikatarsa ta shirya a Accra.

Ken-Ofori-Atta

Ministan ya kara da cewa tattaunawar na tafiya bisa tsari kuma kamar yadda shugaban kasa ya gana da babbar Daraktar IMF Kristalina Georgieva, tattaunawar za ta kasance cikin sauri.

Sai dai masana da masu fashin baki na ganin zai yi wuya gwamnati ta iya cimma wannan burin domin makonni shida suka rage kafin a gabatar da kasafin kudin, kamar yadda mamban kwamitin harkokin kudi na majalisar dokoki Dakta Ato Forson ya bayyana a hirarsa da gidan talabijin din Joy da ke Accra.

Ken-Ofori-Atta da tawaga IMF

Forson ya kuma ce lallai idan hakan ya tabbata, to Ghana za ta kasance 'yar amshin shata ne kawai ga duk dokokin da Asusun zai zayyana. Ya kara da yin kira ga gwamnati akan kada ta yi garaje wajen tattaunawar.

Ra’ayin masani kan harkokin tattalin arziki Hamza Adam Attijjany, bai bambanta da sauran kwararru kan tattalin arziki ba. Ya ce tilas ne Ghana ta shirya fadin gaskiyar yanayin tattalin arzikin kasar, da shirinta na bada aikin yi ga jama’a, da kuma shirinta na biyan basussukan da ake binta na kudi sama da GHC biliyan 400, da hanyoyin da za ta bi wajen biyan basussukan.

Shi kuwa Sarki Imrana Hashiru Dikeni, mai sharhi kan tattalin arziki, cewa yayi ya kamata a sake sabon tsari, duba da cewa ba kasa daya ke bin Ghana bashi ba.

Ghana ta nemi tallafin Asusun Lamuni na Duniya ne bayan da ta shiga matsin tattalin arziki a sanadiyyar annobar coronavirus da tasirin yakin Rasha a Ukraine wanda ya janyo tsananin tsadar rayuwa, lamarin da ya sa kungiyar matsin lamba ta ‘Arise Ghana’ ta gudanar zanga-zanga a watan Yunin 2022.

Saurare rahoton Idris Abdullah Bako a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Shin Ko Ghana Za Ta Iya Cimma Yarjejeniya Da IMF Kafin Ta Gabatar Da Kasafin Kudin 2023?