Shin Kiran Yin Bore Ga India Kan Yankin Kashmir Ya Yi Tasiri?

Firai ministan Pakistan, Imran Khan

Firai minista Imran Khan, ya yi wannan kira ne ga al’umar kasar, domin nuna rashin amincewa da matakin da India ta dauka na karbe ikon cin gashin kan da ta ba yankin Kashmir.

Ga dukkan alamu, kiran da Firai ministan Pakistan ya yi ga al’umar kasar da ta nuna goyon baya ga yankin Kashmir, ta hanyar fitowa kofar gidajensu, da shagunan kasuwancinsu su tsaya na taswon minti 30, bai samu karbuwa ba a jiya Juma’a.

Mafi aksarin jama’ar kasar sun dasa alamar tambaya kan tasirin da wannan mataki zai iya yi.

Firai minista Imran Khan, ya yi wannan kira ne ga al’umar kasar, domin nuna rashin amincewa da matakin da India ta dauka na karbe ikon cin gashin kan da ta ba yankin Kashmir.

Ita dai India ta tura dubban dakarunta zuwa yankin na Kashmir bayan da ta dauki matakin karbe ikon gashin kan da ta ba yankin na Kashmir a bangarenta, ta saka dokar ta-baci, ta rufe gidajen talbijin tare da dakatar da amfani da hanyoyi sadarwa na talho, a matsayin wasu hanyoyin dakile barkewar bore.