Ina Aka Kwana Da Maganar Aikin Wutar Lantarkin Mambilla?

Hoton wata gada a kasar Habasha inda ake aikin samar da wutar lantarki.

Tun mulkin tsohon shugaban Najeriya, Janar Yakubu Gowon aka fara aikin wutar lantarkin na Mambilla, amma har yanzu aikin ya ki ci ya ki cinye wa.

A yanzu dai Ministan lantarki na Najeriya Injiniya Sale Mamman, ya ce zai yi tsayin daka don tabbatar da cewa aikin wutar lantarkin ya kai karshe.

Ya fadi hakan ne a yayin wata hirar da ya yi da wakilinmu Sale Shehu Ashaka.


Mamman, ya ce yanzu ne za a maida hankali kan aikin bayan dogon zamanin da aka dauka a na labarin zane kan ruwa.

Ministan ya ce da ya shigo ya fara aiki bai ga wani abun da aka tabuka a baya kan wutar Mambilla ba, don hatta filin ma sai yanzu ake tsara yadda za a tabbatar da shi don aikin.

Sale Mamman ya ce yana sa ran cewa kafin karshen mulkin gwamnatin Buhari a 2023 za a kammala aikin.

Aikin wutar Mambilla ya faro ne tun zamanin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Yakubu Gowon.

A cewar Janar Gowon cikin wata hirar da ya yi da Muryar Amurka, gwamnatin da ta tunkude shi ce ba ta ci gaba da kokarin da aka yi na yunkurin cimma wannan aiki na gyaran wutar ba.

Aikin wutar lantarkin Mambila dai wani shiri ne da ke karkashin ma’aikatar wutar lantarki wanda ake yi a jihar Taraba da aka kiyasta kammala wa nan da shekarar 2030.

Shiri ne wanda idan an kammala shi zai samar da nauyin wuta Megawatts 3,050 da zai fi kowacce tashar wuta a Najeriya.

An kiyasta cewa aikin zai lashe dala biliyan 5.8.

Saurari wannan rahoton a sauti daga bakin wakilinmu Sale Shehu Ashaka.

Your browser doesn’t support HTML5

Ina Aka Kwana Da Maganar Aikin Wutar Lantarkin Mambilla?